Mai ya kai gemu bakin kwado
Daga Datti Assalafi
BATUN RUFE OFISHIN JAM'IYYAR NNPP A JIHAR BORNO
Labarin da ya karade dandalin Facebook a yammacin nan shine batun rufe ofishin jam'iyyar NNPP da akayi a garin Maiduguri, na sake bin diddigin abinda ya faru, kuma na gano gaskiyar lamari
Ga takarda nan daga hukumar Borno Urban Planning Development Board (BSUPDB), wato hukumar da take da alhakkin kula da tsarin gine-gine a fadin jihar Borno
Sune suka aika da takardan dake dauke da umarnin rufe ofishin jam'iyyar NNPP saboda wai tsarin gurin yana kan tsarin ginin gidaje ne ba ginin shagunan kasuwanci ba, to amma a binciken da na gabatar hakika gurin yana kan tsarin ginin kasuwanci ne da gidaje, ana yin komai a gurin
Kuma tsakanin ofishin jam'iyyar NNPP da jam'iyyar APC mai mulki gini uku ne, don haka a guri daya suke, amma hukumar BSUPDB bata mika takarda don a rufe ofishin jam'iyyar APC mai mulki ba sai na NNPP
BSUPDB tana karkashin umarnin Gwamna ne, don haka anan zamu ce Maigirma Gwamna bai kyauta ba, watakila ya tsorata ne da farin jinin Madugun Kwankwasiyya
NB: Datti assalafi
Allah Ya kyauta
Comments
Post a Comment